Isa ga babban shafi

Afirka Ta Kudu za ta halasta karuwanci don magance cin zarafin mata

Gwamnatin Afirka ta Kudu ta gabatar da shirin halasta karuwanci domin magance manyan laifukan cin zarafi da ake yi wa mata a kasar da ke da yawan masu dauke da cutar kanjamau a duniya.

'Yan sandan Italia sun cafke wata mace da ke sana'ar Karuwanci a kasar Italiya
'Yan sandan Italia sun cafke wata mace da ke sana'ar Karuwanci a kasar Italiya Photo Grain Media
Talla

Ministan shari'ar kasar Ronald Lamola ne ya shaidawa manema labarai matsayar gwamnati na cire  karuwanci ko makamaici daga lissafin masu aikata laifuka kamar yadda yake a halin yanzu.

A cewar sanarwar bayaga magance cin zarafin mata da ya zama ruwan dare a Afirka da Kudu, matakin zai kuma bai wa mata masu zaman kansu damar kula da lafiyarsu akai-akai tare da basu kariya da ingantaccen yanayin gudanar da ayyukansu ba tare da nuna musu wariya ko kyama ba".

Hukumomin kasar dai sun yi la’akari ne da rashin hakuri daga wasu mazajen dake afkawa mata da karfin tsiya, saboda wata kila kiyasin karuwai sama dubu 150 dake fadin kasar a boye suke harkokinsu.

Ministan ‘yan sandan kasar Bheki Cele ya ce an samu karuwar kashe-kashen da ake wa mata tsakanin watan Yuli zuwa Satumba, inda aka kashe mata kusan 1,000, yayin da laifukan fyade ya karu da sama da kashi 11 cikin 100.

Afirka ta Kudu na daya daga cikin kasashe da aka fi samun masu dauke da cutar kanjamau a duniya, nan kuma akafi samun karuwar cin zarafin mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.