Isa ga babban shafi

Faransa na son ta ci gaba da zama yar gaban goshin Cote D'Ivoire

Faransa za ta ci gaba da zama a yar gaban goshin Cote d'Ivoire "a kowane fanni" ciki har da tsaro, kalaman ministar harakokin wajen Faransa Catherine Colonna a ziyarar da ta kai Abidjan a jiya Juma'a.

Alassane OuattaraShugaban kasar Cote D'Ivoire
Alassane OuattaraShugaban kasar Cote D'Ivoire © F24 - RFI
Talla

Muna yaki da nufin kawar da kungiyoyin 'yan ta'adda masu dauke da makamai, da masu fashin saman teku, hade da masu  fataucin mutane, kalaman Ministar harakokin wajen Faransa yan lokuta bayan wata tattaunawa da shugaba Alassane Ouattara a Abidjan.

Ta kara da cewa "Kasashen biyu na tafiya tare,wanda  kuma a shirye suke don tunkarar kalubalen lokutan."

A yau asabar ne ministar ta Faransa za ta gana da ministan tsaro Birahima Ouattara, dan uwan ​​shugaban kasar ta Cote D’Ivoire, domin tattauna batutuwan tsaro da suka shafi dabarun yaki.

Faransa ta girke dakaruntaa Cote d'Ivoire kusan 900, wadanda ke da alhakin tallafawa  ayyukan da ake gudanarwa a Afirka ta Tsakiya da Yammacin Afirka, tare da aiwatar da kawancen soji da Abidjan.

Catherine Colonna ta jaddada cewa, daya daga cikin kalubalen da ke gaban Cote d'Ivoire shi ne ta bi kan hanyar samun ci gaba don tabbatar da wadata, daya daga cikin sharuddan hana matasa fadawa hannun 'yan jihadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.