Isa ga babban shafi

Sama da mutum 9,000 aka yiwa kisan gilla a Yammacin Afirka - Rahoto

Wani rahoto da cibiyoyin kare hakkin bil-adama dake sanya ido akan tashe tashen hankulan da ake fama da su a yankin Afirka ta Yamma, yace akalla mutane 9,823 aka yiwa kisan gilla ta hanyoyi daban daban a yankin a shekarar da ta gabata ta 2021. 

Mutane sun taru a wurin da 'yan bindiga suka harbe mutane da dama a wata mashaya cikin dare a garin Soweto, Afirka ta Kudu.10 ga Yuli, 2022.
Mutane sun taru a wurin da 'yan bindiga suka harbe mutane da dama a wata mashaya cikin dare a garin Soweto, Afirka ta Kudu.10 ga Yuli, 2022. AP - Shiraaz Mohamed
Talla

Rahotan wanda aka saba fitar da shi kowacce ranar 10 ga watan Disamba na kunshe da sanya hannun kungiyar ‘Human Rights Advancement and Development and Advocacy Centre’ (HURIDAC) da ‘African Centre for Democracy and Human Rights Studies’ (ACDHRS). 

Rahoton ya kuma bayyana yadda aka tsare mutane 6,414 ba bisa ka’ida ba, yayin da aka ci zarafi ko jikkata 19,973, sai kuma 48,644 da suka fuskanci cin zarafin dake da nau’i da jinsi. 

Wannan rahoto ya kuma bayyana Najeriya da Nijar da Jamhuriyar Benin a matsayin inda aka samu ci gaba ta fannin kare hakkin bil-adama, sabanin abinda ake gani a kasar Gambia. 

Rahoton ya gabatar da teburin kasashen da suka fi mutunta hakkin Bil Adama wanda ya sanya Jamhuriyar Benin a sahun gaba, sai kuma Mali da Cape Verde a matakin karshe. 

Ayodele Ameeen, Daraktan HURIDAC yace rahotan nasu ya mayar da hankali ne akan alkaluman kare hakkin Bil Adama na shekarar 2021, abinda yace an samu koma baya a kasashen dake Afirka ta Yamma da dama. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.