Isa ga babban shafi

Amurka na neman inganta alakarta da kasashen Afirka

A ranar Talata ne shugaban Amurka Joe Biden zai jagoranci taro da shugabannin kasashen Afrika karo na biyu, wanda ke zuwa a dai-dai lokacin da kasashen China da Rasha ke samun karbuwa a nahiyar.

Shugaban Amurka Joe Biden kenan
Shugaban Amurka Joe Biden kenan © Marca
Talla

Taron na kwanaki uku, zai duba karin jarin da Amurka ke son zubawa a nahiyar da kuma gudun mowarta wajen samar da abinci ta hanyar nuna illar da mamayar Rasha a Ukraine ta haifar.

Taron zai kuma dubu irin gudun mowar da Amurka za ta baiwa kasashen a bangaren dimokaradiya da gudanarwar gwamnati ta gari da kuma yadda za su tunkari matsalar sauyin yanayi.

Shugaba Biden ya kuma nuna goyon bayansa ga nahiyar Afrika wajen samun kujera a majalisar tsaro ta MDD da kuma ganin nahiyar ta samu wakilci a kungiyar G20.

Tuni dama dai shugabannin kasashen Afrika ke gudanar da taro da kasar China da wasu kasashe abokan huldar Amurka irin su Faransa da Birtaniya da Japan da kuma kungiyar Tarayyar Turai duk bayan shekararu uku.

China wacce ita ce babbar abokiyar hamayyar Amurka ta zuba jari sosai a Afrika kusan ninki biyu na wanda Amurka ta yi.

Amurka dai ta gayyaci dukkanin shugabanin kasashen da ke bin tsarin doka, in banda wadanda aka kwaci mulki a cikin su duk kuwa da cewa suna da alaka da kasar irin su Burkina Faso da Guinea da Mali da kuma Sudan, yayin da kasar Eritrea da ke karkashin shugancin kama-karya aka hana ta katin gayyata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.