Isa ga babban shafi

Tarayyar Afirka na kokarin soke takardar visa a tsakanin kasashen nahiyar

Tafiye tafiye a Afirka sun kasance masu sauki ga 'yan Afirka a cikin shekara ta 2022, tare da ƙarancin ƙuntatawa. Wannan shi ne sakamakon sabon rahoton da ya shafi harakokin shige da fice a Afirka, wanda bankin raya Afirka da hukumar Tarayyar Afirka suka rubuta tare.

ABDALLAH UMARU  Masanin harakokin shige da fice
ABDALLAH UMARU Masanin harakokin shige da fice © rfi hausa
Talla

Kokarin da kungiyar Tarayyar Afirka ke yi don soke takardar visa a tsakanin kasashen nahiyar na ci gaba da fuskantar cikas, domin kuwa adadin kasashen da ke aiwatar da wannan tsari bai wuce 27% ba.

Alkalumma na nuni da cewa kasashen Benin, Gambia da kuma Seychelles ne suka fi bayar da kyakkyawan misali game da wannan shiri. Marubutan sun ba da haske, musamman, gaskiyar cewa duk da kulle-kulle saboda barkewar cutar ta Covid-19 da rushewar balaguron , “kashi 93% na ƙasashen Afirka sun kiyaye ko haɓaka maki idan aka kwatanta da 2021”. Don haka, kashi biyu bisa uku na kasashen Afirka sun amince da manufofin biza masu sassaucin ra'ayi fiye da shekaru shida da suka gabata.

Abdallah Umaru, dan Nijar mazauni jamhuriyar Benin, ya bayyana mahangarsa a game da shirin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.