Isa ga babban shafi

Gwamnatin Gambia ta ce an dakile wani yunkurin juyin mulki

Gwamnatin Gambia ta ce ta dakile yunkurin juyin mulkin da aka shirya yi a ranar Talata tare da cafke sojoji hudu.

Shugaba Adama Barrow na kasar Gambia kenan
Shugaba Adama Barrow na kasar Gambia kenan AFP/File
Talla

Sanarwar da gwamnatin ta fitar ta ce an samu nasarar shawo kan al’amarin yanzu haka, tare da fadada binciken wadanda suke da hannu a lamarin.

Kawo yanzu dai babu wani tabbaci daga wasu majiyoyi da ake zargin suna da hannu a lamarin.

Rahotannin sun ce sojoji sun yi ta yawo a kusa da hedkwatar fadar shugaban kasar da ke tsakiyar Banjul babban birnin kasar a yammacin ranar Talata, kuma an yi ta yada jita-jita a cikin dare kan yiwuwar juyin mulkin.

"Bisa bayanan sirri da ke nuna cewa wasu sojojin kasar Gambiya na shirin hambarar da gwamnatin shugaba Adama Barrow ta dimokuradiyya, a wani samame da sojoji suka yi cikin gaggawa a jiya sun kama wasu sojoji hudu da ke da alaka da wannan yunkurin juyin mulki," in ji gwamnati.

“Sojojin da aka kama a halin yanzu suna taimakawa ‘yan sandan wajen gudanar bincikensu.

A halin da ake ciki kuma, sojojin na ci gaba da neman wasu mutane uku da ake zargi da hannu a ta’asar.

Kasar da ke yankin Afirka ta Yamma, na karkashin mulkin dimokradiyya mai cike da rauni, inda har yanzu take fama da sakamakon mummunan mulkin kama-karya na shekaru 22 a karkashin Yahya Jammeh.

Jammeh dai ya sha kaye a zaben shugaban kasa a watan Disambar 2016 a hannun Adama Barrow, inda ya tsere zuwa Equatorial Guinea.

An sake zaben Barrow a watan Disambar 2021 a karo na biyu na shekaru biyar da kashi 53 na kuri'un da aka kada.

Yammacin Afirka dai ya girgiza sakamakon juyin mulkin soji tun daga shekarar 2020, a kasashen Mali, Guinea da kuma na baya-bayan nan a Burkina Faso.

Ana danganta juyin mulkin, da matsalar masu tayar da kayar baya da ta kunno kai a yankin Sahel, abin da ya sa shugabannin kungiyar ECOWAS a wannan watan suka yanke shawarar kafa rundunar shiga tsakani domin karfafa zaman lafiya a nahiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.