Isa ga babban shafi

Shugaba Tshisekedi na Congo na fuskantar matsin lamba kan matsalar tsaro

Wasu fitattun mutane uku a Congo ciki har da wanda ya lashe kyautar Nobel Denis Mukwege, sun zargi shugaban kasar Felix Tshisekedi da kokarin jefa kasar cikin mawuyacin hali ta hanyar shigo da kasashen waje domin tunkarar matsalar tsaro.

Shugaba Felix Tshisekedi
Shugaba Felix Tshisekedi © RFI/France 24
Talla

A wata alama da ke nuna karuwar matsin lamba kan Tshisekedi kan gabacin DR Congo da ke fama da rikici, mutane ukun sun ce kasar da ta kasance mafi girma a yankin kudu da hamadar sahara ta fuskanci rarrabuwar kawuna.

Baya ga Mukwege, wanda ya kasance likitan mata  wato mutumin da ya ci kyautar Nobel ta zaman lafiya ta shekarar 2018, saboda aikin da ya yi wajen taimaka wa matan da aka yi musu fyade, wani dan siyasa Martin Fayulu ne ya sanya hannu a sanarwar, wanda ya sha kaye a hannun Tshisekedi a zabukan 2018 mai cike da cece-kuce.

Kungiyoyin da ke dauke da makamai sun yi ta yawo a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, wadanda yawancinsu sun fito ne daga yankuna biyu da yaki ya barke musu a karshen karnin da ya gabata.

Ta'addancin baya-bayan nan dai ya shafi wata kungiya mai dauke da makamai da ake kira M23, wacce ta kwace yankuna da dama a lardin Kivu ta Arewa.

Yayin da dakarun Congo ke ci gaba da yaduwa, Tshisekedi ya yi kira ga wata kungiyar kasashe bakwai, wato EAC, da ta tura sojoji zuwa kasar.

Kungiyar ta EAC dai ta kunshi kasashen Rwanda da Uganda, wadanda suka dade suna zargin tada rikici a gabashi.

Tshisekedi ya gaji Joseph Kabila, wanda ya yi mulki tun shekara ta 2001.

Sai dai a zaben na wancan lokaci na cike da zarge-zargen magudi, kuma Fayulu ya dage cewa shi ne halastaccen shugaban kasa, inda ya ce sama da kashi 60 na kuri’un da aka kada nasa ne.

Tshisekedi, Fayulu da Matata sun riga sun bayyana aniyarsu ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben da za a gudanar ranar 20 ga Disamban 2023.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.