Isa ga babban shafi

Wani sojan Uganda ya kashe abokan aikinsa uku a Somalia

Wani sojan Uganda ya harbe wasu abokan aikinsa guda uku da ke aiki a Somaliya karkashin rundunar wanzar da zaman lafiya ta Tarayyar Afirka.

Sojojin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo kenan, yayin sintiri a kusa da Semuliki da ke cikin gandun dajin Virunga a ranar 14 ga Disamba, 2021.
Sojojin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo kenan, yayin sintiri a kusa da Semuliki da ke cikin gandun dajin Virunga a ranar 14 ga Disamba, 2021. AFP - SEBASTIEN KITSA MUSAYI
Talla

Kakakin Rundunar Sojojin Uganda Birgediya Janar Felix Kulayigye ya ce sojan ya yi barin wuta ga abokan aikinsa da safiyar Litinin, kuma dukkanin mutanen hudun dai na na gadin filin tashi da saukar jiragen sama na kasa da kasa da ke Mogadishu babban birnin kasar Somaliya.

"Muna tunanin ko yana da tabin hankali," in ji Kulayigye, ya kara da cewa sojojin Uganda sun kafa kwamitin bincike don gano musabbabin harbe-harben.

Ya ce an kama sojan kuma za a garzaya da shi Uganda domin fuskantar kotun soji.

Tun shekara ta 2007 ne Uganda ke da sojoji a Somaliya domin yakar 'yan tawayen Somaliya da ke neman hambarar da gwamnati a Mogadishu.

Kasashen Kenya da Burundi da Djibouti da kuma Habasha su ma suna da sojoji tare da tawagar wanzar da zaman lafiya ta Tarayyar Afirka a Somaliya.

Harbin na karshe da ya shafi sojojin Uganda a Somaliya ya faru ne a watan Mayun 2019 lokacin da wani soja ya harbe wani babban jami'i kafin ya kashe kansa.

A shekarar 2017, asibitin kula da masu tabin hankali na kasar Uganda ya bude wani sashe da zai taimaka wa sojoji, musamman wadanda suka yi aiki a Somaliya, don shawo kan matsalar damuwa da suka samu sakamakon yadda sojoji ke kashe mutane a wuraren taruwar jama'a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.