Bayan da Mali ta sallame su, sojojin Cote d'Ivoire 46 sun koma gida
Bayan da shugaban Mali Assimi Goita ya yi musu afuwa, sojoji 46 ‘yan asalin kasarcote d’Ivoire wadanda aka yanke wa hukuncin dauri a gidan yari, sun isa birnin Abidjan a yammacin jiya asabar.
Wallafawa ranar:
Sojojin dai sun share tsawon watanni 6 tsare a hannun mahukuntan kasar Mali, bayan da aka bayyana cewa sun shiga kasar ne a matsayin sojin haya, yayin da daga bisani kotu ta yi zama tare da yanke musu hukuncin daurin shekaru 20 kowanne tare da biyan tare da ta kudi cfa milyan biyu.
Wata majiya ta ce, kafin isa birnin Abidjan, sojojin sun yada zango a kasar Togo domin ganawa da shugaba Faure Gnasingbe wanda ya shiga tsakanin domin warware wannan takaddama tsakanin Mali da Cote d’Ivoire.
Yayin da isarsu a birnin Abidjan kuwa, shugaba Alassan Ouattara ya gana da sojojin, tare da jinjina wa kokarin da kasashe aminai suka yi domin ‘yantar da wadannan sojoji. Hakazalika, Ouattara a jawabin nasa, ya bayyana Mali a matsayin kasa aminiya ga Cote d’Ivoire.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu