Isa ga babban shafi

Hatsarin mota ya kashe mutum 40 a Senegal

Akalla mutane 40 ne suka mutu, wasu da dama kuma suka jikkata bayan da wasu motocin bas guda biyu suka yi karo kusa da garin Kaffrine da ke tsakiyar kasar Senegal a ranar Lahadi, a cewar hukumomin kasar.

Motar da ta yi hatsari a Kaffirne da ke tsakiyar Senegal kenan, ranar 8 ga watan Janairun 2023.
Motar da ta yi hatsari a Kaffirne da ke tsakiyar Senegal kenan, ranar 8 ga watan Janairun 2023. AFP - CHEIKH DIENG
Talla

Shugaba Macky Sall ya ba da sanarwar kwanaki uku na zaman makoki daga ranar Litinin.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na twitter ranar Lahadi ya kuma ce an samu mutuwar mutane 40 da kuma inda da dama suka samu munanan raunuka.

A wata sanarwa da mai shigar da kara na Senegal ya fitar ya ce mutane 38 ne suka mutu da farko, inda aka samu karin mutum biyu daba bisani.

Mai gabatar da kara, Cheikh Dieng, ya ce binciken farko ya nuna cewa hatsarin ya faru ne a lokacin da wata motar bas dauke da fasinjoji ta kwace, biyo bayan fashewar wata tayar, kafin ta yi karo da wata motar bas kuma.

Kanal Cheikh Fall, wanda ke kula da ayyuka na hukumar kashe gobara ta kasar da ke yammacin Afirka, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa mutane 38 ne suka mutu yayin da 87 suka jikkata a hatsarin.

A watan Oktoban shekarar 2020, akalla mutane 16 ne suka mutu, wasu 15 kuma suka jikkata, lokacin da wata motar bas ta yi karo da wata babbar motar dakon kaya a yammacin kasar Senegal.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.