Isa ga babban shafi

An kaddamar da ranar 'kishin kasa' a Mali

Shugaban gwamnatin sojin Mali Asimi Goita ya kaddamar da ranar kishin kasa, wadda za ta zama tamkar wata ranar kara zaburar da jama’a game da muhimmancin kishin kasa da kuma yaki da katsalandan da kasashen waje ke yi musu kan harkokin cikin gida. 

shugaban gwamnatin sojin Mali Assimi Goita.
shugaban gwamnatin sojin Mali Assimi Goita. © AFP
Talla

 

Kaddamar da ranar da za’a rinka bikin zagayowar ta duk shekara, na zuwa ne bayan wata zanga-zangar kin jinin katsalandan din Turawa da ‘yan kasar suka yi ta hanyar kona tutar kungiyar Tarayyar Turai, yayin da suke adawa da karin takunkuman da kungiyar ECOWAS ko CEDEAO ta sake lafta wa kasar saboda shirin sojojin na tsawaita wa’adin mulkin su zuwa shekaru 5 nan gaba. 

Jagororin gwamnatin dai a baya sun yi alkawarin mika Mulki ga farar hula a watan Maris na shekarar 2024, sai dai a yanzu sun kara wa’adin  zuwa shekaru biyar, suna masu kafa hujja da nasororin da ake samu wajen inganta tsaro a kasar duk da dai manyan hukumomi na ci gaba da musanta hakan, ciki har da majalisar dinkin duniya. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.