Isa ga babban shafi

Mataimakin shugaban kasar Gambia ya mutu

Mataimakin shugaban Gambia, Badara Joof ya rasu bayan ya yi fama da  gajeriyar jinya a wani asibiti da ke kasar India.

Mataimakin shugaban kasar Gambia, Badara Joof da ya rasu a India.
Mataimakin shugaban kasar Gambia, Badara Joof da ya rasu a India. © moherst.gov.gm
Talla

Shugaban Gambia, Adama Barrow, shi ne ya sanar da mutuwar mataimakin nasa a wani sako da ya aika a shafinsa na Twitter, yana mai bayyana alhininsa ga al’ummar kasar kan wannan rashi da suka yi, amma bai yi karin haske ba game da rasuwar.

Mista Joof mai shekaru 65,  ya rasu ne makwanni uku da balaguronsa zuwa India domin neman magani kan wata larura da yake fama da ita kamar yadda rahotanni ke cewa.

Shugaba Barrow ya nada Joof ne a matsayin mataimakinsa bayan ya sake lashe zabe a watan Disamban 2021.

Marigayi Joof dai, kwararren malamin harshen Ingilishi ne kafin daga bisani ya zama sakataren din-din-din a ma’aikatar ilimin kasar na tsawon shekaru.

Kazalika ya yi aiki a matsayin wakilin Babban Bankin Duniya a Gambia, inda kuma a shekarar 2014, bankin duniyar ya nada shi a matsayin wakilinsa na bangaren bunkasa ilimi a kasar Senegal.

A ranar 22 ga watan Fabairun 2017 ne, shugaba Barrow ya dauko shi ya nada shi ministan ilimin manyan makarantu da bincike, kimiya da fasaha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.