Isa ga babban shafi

Wasu kasashe 40 sun bukaci Isra'ila ta dage takunkumin da ta kakabawa Falasdinawa

Wasu kasashen duniya 40 sun yi kira ga Isra'ila da ta dage takunkumin da ta kakabawa hukumar Falasdinu a farkon wannan wata saboda yunkurin da ta ke yi na ganin babbar kotun Majalisar Dinkin Duniya ta saurari kan mamayar Isra'ila.

Wasu likitoci a yankin al-Shifa dake Gaza, 6/08/2022.
Wasu likitoci a yankin al-Shifa dake Gaza, 6/08/2022. © MAHMUD HAMS/AFP
Talla

A ranar 30 ga watan Disamba ne babban taron Majalisar Dinkin Duniya ya gabatar da wani kuduri da ke neman jin ra'ayin kotun duniya kan batun mamayar da Isra'ila ke yi a yankunan Falasdinawa.

A wani mataki na ramuwar gayya, a ranar 6 ga watan Janairu, Isra’ila ta sanar da kakaba wasu jerin takunkumai, ciki har da na kudi kan hukumar Falasdinu, saboda matsawa kan kudurin na neman hakkinta.

A cikin wata sanarwa ga manema labarai ranar litinin, wasu kasashe 40 na Majalisar Dinkin Duniya, wadanda ke jaddada goyon bayansu ga kotun ICJ da kuma dokokin kasa da kasa, sun bayyana matukar damuwa dangane da matakin da gwamnatin Isra'ila ta dauka na matsawa al'ummar Palasdinu, shugabanni da kungiyoyin fararen hula.

Kashen da suka goyi baya da akasi

Sanarwar na dauke da sa hannun kasashen da suka kada kuri'ar amincewa da wannan kudiri da suka hada da Algeria, Argentina, Belgium, Ireland, Pakistan da Afirka ta Kudu, da dai sauransu, sai dai kuma - Japan, Faransa da Koriya ta Kudu sun kaurace wa zaman kada kuri'ar – yayin da kasashen irinsu Jamus da Estonia suka zabi zama ‘yan baruwanmu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.