Isa ga babban shafi

Ivory Coast ta karrama sojinta da Mali ta kama su

Ivory Coast ta karrama sojojinta 49 da  lambar yabo mafi girma bayan gwamnatin Mali ta tsare su tsawon watanni shida, lamarin da ya haddasa zazzafar tankiyar diflomasiya tsakanin kasashen biyu na yammacin Afrika. 

Shugaban Cote d'Ivoire Alassane Ouattara yayin maraba da sojojin kasar arba'in da shida da sojojin Mali suka yi wa afuwa, yayin da suka isa filin jirgin saman Felix Houphouet Boigny na kasa da kasa da ke Abidjan, Ivory Coast Janairu 7, 2023.
Shugaban Cote d'Ivoire Alassane Ouattara yayin maraba da sojojin kasar arba'in da shida da sojojin Mali suka yi wa afuwa, yayin da suka isa filin jirgin saman Felix Houphouet Boigny na kasa da kasa da ke Abidjan, Ivory Coast Janairu 7, 2023. © REUTERS/Luc Gnago
Talla

Tun a cikin watan Yulin bara ne, gwamnatin Mali ta kama tare da tsare sojojin na Ivory Coast jim kadan da isar su filin jiragen sama na birnin Bamako. 

Gwamnatin Mali ta zargi sojojin  da zama dakarun haya masu leken asiri, amma Ivory Coast da Majalisar Dinkin Duniya sun ce, sam ba haka ba ne, domin sun isa kasar ne da zummar mara baya ga sojojin Jamus da ke aikin wanzar da zaman lafiya karkashin shirin Majalisar Dinkin Duniya a kasar. 

A ranar 30 ga watan Disamban da ya  gabata ne, wata kotu a birnin Bamako ta yanke wa wadannan sojoji hukuncin daurin shekaru 20 kowannensu a gidan yari. 

Sai dai daga bisani, gwamnatin sojin Malin karkashin jagorancin Kanar Asimi Goita   ta yi musu afuwa a ranar 6 ga watan Janairu da muke ciki. 

An dai karrama sojojin ne a wani biki da ya guda a Talatar nan da lambar jarumta mafi girma a kasar ta Ivory Coast.  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.