Isa ga babban shafi

An yi arangama tsakanin Sojin Rwanda da 'yan sandan Congo a lardin Kivu

Wata arangama tsakanin dakarun Rwanda da 'yan sandan Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo a wani karamin tsibiri da ke yankin Kivu na gabashin kasar ya ta'azzara faragaba, duba da yadda kasashen biyu ke yi wa juna kallon hadarin kaji a game da matsalar 'yan tawayen M23. 

Wasu Sojojin Congo a lardin arewacin Kivu.
Wasu Sojojin Congo a lardin arewacin Kivu. AFP PHOTO / JUNIOR D. KANNAH
Talla

Wata majiyar rundunar sojin ruwan Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta ce 'yan sandan da aka girke a tsibirin Ibindja da ke gabashin kasar ne suka kalubalanci wasu kanan jiragen ruwa 3 da ke dauke da dakarun Rwanda a yayin da suke hanyar zuwa sansaninsu a ranar Asabar. 

Majiyar ta ce a yayin da 'yan sandan suke nemi in dalilin da ya sa suka keta kan iyakar Congo ne aka yi ta zare wa juna ido, har ya kai ga musayar wuta, lamarin da ya tsorata al'umomin da ke kauyen Chivumu. 

 Wakilin wata kungiyar farar hula a yankin, Jackson Kilamba ya ce hatsaniyar ta sa iyalai a tsibirin sun tsere, inda suka nemi mafaka a gabar kogin Birava. 

Rahotanni sun ce kura ta lafa har ma dakarun Rwanda sun koma sansaninsu ba tare da sun sauka a tsibirin ba, sai dai wani jami'in dan sandan Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ya samu raunin harbin bindiga. 

Har yanzu babu wani bayani daga mahukuntan Rwanda a game da wannan lamari. 

Ana zaman tankiya tsakanin makwaftan biyu, sakamakon sake bullar kungiyar 'yan tawayen M23 na 'yan kabilar Tutsi, wanda Congo ke zargin Rwanda na mara wa baya. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.