Isa ga babban shafi

Kotun Kamaru ta daure tsohon makusancin Paul Biya shekaru 30 a kurkuku

Kotun hukunta manyan laifuka ta musamman a kasar Kamaru ta yanke wa wani tsohon makusaci ga shugaban kasar Paul Biya tsohon ministan tsaro Edgar Alain Mebe Ngo'o, daurin shekaru talatin a gidan yari.

Alamar zartar da hukuci
Alamar zartar da hukuci © Getty Images/ Romilly Lockyer
Talla

Ngo’o wanda kuma tsohon shugaban ma’aikatar fadar shugaban kasar ne ya kwashe sama da shekaru 4 a kurkuku da shi da uwargidansa, an kamashi da laifin almubazzaranci da fiye da CFA biliyan 23.

Mai dakinsa Bernadette Mebe Ngo'o, wadda ita ma aka tsare ta a gidan yari tun a watan Maris na 2019, an yanke mata hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari saboda almubazzaranci sama da CFA miliyan 310.

Lauyan Mebe Ngo’o, Pauline Noël Koe Amougou ta sanar da daukaka kara nan take tare da nuna takaicin ta kan hukuncin kotun da tace umurni ne.

Wasu na kallon tsare Ngo’o mai shekaru 66 amatsayin yaki ne a Yaounde tsakanin masu neman gadon shugaban kasar Paul Biya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.