Isa ga babban shafi

Wani dan Najeriya da aka samu da laifin yiwa sojojin Danemark barazana ya nemi mafaka

Wani dan Najeriya da kotun kasar Danemark ta samu da laifin jefa rayuwar sojoji cikin hadari a wani harbi da aka yi a mashigin tekun Guinea da ake zargin dan fashin teku ne ya nemi mafaka a kasar Scandinavia..

Wani dan Fashin teku da ake tsare da shi
Wani dan Fashin teku da ake tsare da shi AFP - PUNIT PARANJPE
Talla

Hukumomin Danemark sun mayar da wannan mutum mai shekaru 41, wanda ya bayyana kansa a matsayin Lucky saboda dalilai na jin kai, sannan kuma suka yi masa shari'ar aikata laifukan da suka faru a cikin ruwan kasa da kasa a gabar tekun Najeriya.

A yammacin ranar 24 ga Nuwamba, 2021, wasu da ake zargin 'yan fashin teku ne a cikin wani kwale-kwale suka fara bude wuta kan wani jirgin sama mai saukar ungulu na sojojin ruwan Denmark da ke sintiri don hana ayyukan sata saman teku.

An kashe hudu da ake zargin ‘yan fashin teku ne, na biyar da ya fada cikin ruwa sannan sojojin Denmark suka kama wasu uku sannan aka sako su a teku, a cewar hukumomin Danemark.

A gefe guda kuma, Lucky ya kasance a hannun sojojin Danemark,saboda an same shi a daidai wurin da rikicin ya faru, bayan da ya samu rauni a kafar hagu a yayin musayar wuta.

An ɗauke shi zuwa Denmark, an yanke masa hukunci amma ba a yanke masa hukuncin ɗaurin kurkuku ba.

"Idan na koma Afirka, ina bukatar in zama mai karfi, don samun makoma. Dole ne ku iya yin aiki tukuru idan kuna son tsira, kuma ba zan iya yin hakan a yanzu ba," Kucky na fadar haka ne yayin wata ganawa da wani gidan talabijen mai zaman kan sa.

Mashigin tekun Guinea mai nisan kilomita 5,700 daga Senegal zuwa Angola, ya samu raguwar fashin teku sakamakon hadin gwiwar kasashen da ke gabar teku da kasashen Turai.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.