Isa ga babban shafi

Mata a DRC na bukatar gwamnati ta fatattaki M23 daga arewacin Goma

Daruruwan mata a jamhuriyar Dimokradiyyar Congo sun kwarara kan tituna tare da zanga-zangar bukatar mayakan M23 su fice daga birnin Goma na gabashin kasar.

Shugaban Congo Felix Tshikedi
Shugaban Congo Felix Tshikedi © Arsène Mpiana / AFP
Talla

Matan sun koka game da yadda zaman mayakan a cikin birnin ke haddasa musu wahala a rayuwar su baya ga tsananin yunwa da kuma hana yaransu zuwa makaranta.

Matan da fiye da rabin su ke goye da yara a bayan su, sun bukaci gwamnatin kasar ta dauki matakin gaggawa kan fadaduwar ayyukan mayakan, yayin da suke rewa wakokin da ke bayyana irin halin yunwa da bakin talauci da rikicin ya jefa su a ciki.

Yakin da yankin gabashin Goma ya shafe shekaru yana fama da shi na ci gaba da jefa fararen hula cikin halin kakanikayi.

Bayanai sun ce a yankin na Goma kadai akwai kungiyoyin masu rike da makamai sama 100, abinda masana ke ganin zaman su a yankin na da alaka da albarkatun kasa da ke kwance a yankin musamman Gwal.

Kawo yanzu dai yakin ya tafi da dubban rayuka da kuma raba miliyoyi da muhallan su, yayin da a watan Disamban da ya gabata kadai Majalisar dinkin duniya ta ce ‘yan tawayen sun kashe mutane 130 a cikin kauyuka biyu da suka tasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.