Prime ministan Mali ya dakatar da ziyara a arewacin kasar saboda matsalar tsaro
Prime ministan Mali Choguel Kokalla Maiga ya dakatar da ziyarar sa a yankin arewacin kasar sakamakon barazanar matsalolin tsaro.
Wallafawa ranar:
Maiga mai shekaru 64 ya isa birnin Gao a ranar juma’ar da ta gabata a ziyarar aiki ta kwanaki 4, yayin da cikin ziyarar aka tsara zai ziyarci garuruwan Bourem da Ansongo.
A yanzu dai an dakatar da ziyarar garuruwan biyu, saboda rahotannin ta’azzarar hare-haren ‘yan ta’adda, kamar yadda guda daga cikin kusoshin gwamnatin kasar ya shaidawa kamfanin dillacin labaran Faransa AFP.
Magajin garin Bourem Hamadou Mahammane Toure ya tabbatarwa da manema labarai soke ziyarar, wadda ke zama karon farko da Prime ministan ya kai arewacin kasar tun watan Disamba, bayan fama da cutar shanyewar barin jiki.
A yayin ziyarar dai an shirya Maiga zai tattauna da shugabannin al’umma da sojojin dake bakin daga, sannan kuma zai rabawa manoma kayayyakin aikin gona da nufin rage musu radadin ayyukan ta’addancin, yayin da zai kaddamar da wasu ayyukan ci gaba a yankunan, wadanda gwamnati ta samar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu