Isa ga babban shafi

MDD ta dakatar da ayyukan jin kai a Jamhuriyar Congo

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa ta dakatar da ayyukan jin kai a mafi yawan yankunan gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, bayan an kai wa daya daga cikin jiragenta hari.

'Yan tawayen M23 da wani rahoton Amnesty International da ya ce an kashe gomman mutane a watan Nuwambar 2022.
'Yan tawayen M23 da wani rahoton Amnesty International da ya ce an kashe gomman mutane a watan Nuwambar 2022. © James Akena/Reuters
Talla

 

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun harbo wani jirgin sama mai saukar ungulu na Majalisar Dinkin Duniya daga cibiyar kasuwanci ta Goma da ke lardin Kivu ta Arewa a ranar Juma’a, a cewar ofishin kula da ayyukan jin kai na MDD OCHA, mai dauke da fasinjoji 10 da ma'aikatan jirgin uku.

Fasinjojin 10 da ma'aikatan jirgin uku da ke cikin jirgin ba su samu rauni ba, amma hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta yanke shawarar dakatar da ayyukan jin kai na wani dan lokaci a Arewacin Kivu da lardin Ituri da ke makwabtaka da su.

Gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo na fama da kalubalen tsageru, sakamakon yake-yaken da suka barke a farkon karni na 21.

Wata kungiyar 'yan tawaye ta M23, ta kwace yankuna da dama a arewacin Kivu tun daga karshen shekarar 2021, kuma tana dab da kame yankin Goma, wani birni mai mutane sama da miliyan daya da ke kan iyaka da Rwanda.

Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo dai na zargin makwabciyarta Rwanda da marawa kungiyar baya, zargin da Amurka da wasu kasashen yammacin duniya da dama da kuma Majalisar Dinkin Duniya suka amince da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.