Isa ga babban shafi

Jarumin fim din Hotel Rwanda ya shaki iskar 'yanci

Mahukuntan Rwanda sun sanar da sakin jarumin fitaccen Fim din nan mai suna Hotel Rwanda daga gidan yari, inda aka yanke masa hukuncin shekaru 25, saboda laifin ta’addanci. 

Jarumin fim din Hotel Rwanda kenan, Paul Rusesabagina.
Jarumin fim din Hotel Rwanda kenan, Paul Rusesabagina. © AP - Muhizi Olivier
Talla

Kakakin gwamnatin kasar Yolande Makolo ne ya bayyana wa manema labarai hakan, yana mai cewa an yanke hukuncin ne bayan da shi Paul Rusesabagina, ya nemi afuwar hukuncin da aka yanke masa. 

A cewar Makolo, kafin yanke hukuncin sai da aka tattauna da dukannin masu ruwa da tsaki da kuma wasu kasashen turai da suka hada da Amurka da Qatar. 

Ana saran Rusesabagina zai hadu da Iyalansa a ranar Asabar. 

Kaffin isowar sa Rwanda dai za’a fara kai shi birnin Doha na kasar Qatar, daga bisani a wuce da shi Amurka, sannan kuma zuwa ga iyalan nasa. 

A bisa kididdiga dai Rusesabagina mai shekaru 68 yanzu ya shafe kwanaki 939 a gidan yari, kuma tarihi ya nuna ce wa, ya karbi lambar girmamawa ta nuna tausayi lokacin da ya ceci mutum 1,200 a lokacin kisan kare dangin Rwanda da aka yi a 1994, lokacin ya na aiki a wani Otal. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.