Isa ga babban shafi

Wani dan Afrika ta Kudu ya zarce shekaru 5 a hannun 'yan ta'adda a Mali

Iyalan wani dan kasar Afrika ta Kudu da masu ikirarin jihadi suka yi garkuwa da shi a Mali tsawon shekaru 5 kenan yanzu sun sake yin kira a sake shi ‘yan kwanaki bayan da aka saki dan jaridar nan bafaranshe, Oliver Dubois.

Tun a shekarar 2012 'yan ta'adda suka fara cin karensu babu babaka a arewacin Mali.
Tun a shekarar 2012 'yan ta'adda suka fara cin karensu babu babaka a arewacin Mali. REUTERS
Talla

An sace Gerco van Deventer,  maai shekaru 47 ne ranar 3 ga watan Nuwamban shekarar 2017 a Libya, a kan hanyarsa ta zuwa wata tashar wutar lantarki da ake ginawa a kudancin babban birnin kasar Tripoli.

Wasu injiniyoyi 3 ‘yan kasar Turkiya da aka sace su tare sun samu ‘yancinsu bayan watanni 7, amma Van Deventer ya ci gaba da zama a hannun ’yan ta’addan, inda suka canza mai wuri zuwa Mali.

Mai dakinsa, Shereen Deventer ta  bayyana yadda iyalansa ke matukar bukatar ganin sa a tare da su a gida, tana mai cewa ‘yayansa 3 na kewar sa.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, dan jaridar nan da kwanan ‘yan ta’adda suka sake shi, Olivier Dubois ya ce ya shafe kusan shekara  guda da Deventer a hannun ‘yan ta’adda a Mali, yana rokon shi ma a sake shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.