Isa ga babban shafi

Ma'aikatan jirgin ruwa 16 sun yi batan dabo a tekun Guinea

‘Yan fashin teku sun yi awun gaba da wani jirgin ruwan dakon mai na kasar Laberiya a mashigin tekun Guinea, inda rahotanni ke cewa, ma’aikatan jirgin su 16 sun yi batan dabo.

Sojojin ruwan Najeriya yayin sintiri a mashigar ruwan tekun Guinea.
Sojojin ruwan Najeriya yayin sintiri a mashigar ruwan tekun Guinea. © AP Photo/Sunday Alamba
Talla

Jirgin, mallakar kamfanin Monjasa Reformer, mai tsawon mita 135 ya fuskanci agaji na gaggawa ranar Asabar a tsakiyar ruwa, wato nisan mil 160 kwatankwacin kilomita 260 a yammacin Port Pointe-Noire da ke Jamhuriyar Congo.

Kamfanin jirgin ya tabbatar da cewa ma’aikatan jirgin sun nemi mafaka a cikin wani daki da aka kebe, wato lokacin da ‘yan fashin suka shiga cikin jirgin, bisa ka’idojin gaggawa na yaki da fashi da makami.

Monjasa ya ce "A halin yanzu, hanyoyin sadarwa na cikin jirgin sun lalace kuma muna aiki tare da hukumomin yankin don samar da sadarwa don fahimtar halin da ake ciki a cikin jirgin tare da ba da duk wani tallafi da ma'aikatan jirgin ke bukata don shawo kan wadannan munanan abubuwan.”

Kamfanin ya ce jirgin ya tsaya ne lokacin da lamarin ya faru, amma ya ki bayar da bayanai kan kasashen da ma’aikatan jirgin suka fito.

A cewar wani jami'i a tashar ruwan Pointe-Noire, jirgin ya isa ruwan Congo ne a ranar 18 ga watan Maris kuma ya tashi a ranar 22 ga Maris, amma ya shiga ruwan da ke yankin kasa da kasa lokacin da aka kai masa hari.

Jami'in ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa "Mutane uku ne suka mamaye jirgin kuma tun daga lokacin ba a ji duriyar ma'aikatan jirgin ba."

'Yan fashin teku sun dade suna kai hari a mashigin tekun Guinea, babban hanyar jigilar kayayyaki da ke da nisan kilomita 5,700 daga Senegal zuwa Angola, inda wasu kungiyoyin 'yan ta’adda na Najeriya ke kai hare-hare.

Sai dai tun daga shekarar 2021, masu safarar jiragen ruwa sun ce 'yan fashin teku na kara kai hare-hare a cikin ruwan da ke yankin kasa da kasa.

Hare-haren su ya sanya ma’aikatan jirgin ruwa da kamfanonin jiragen ruwa kiraye-kirayen ya kamata a kara karfin sojan ruwa na kasashen waje, domin dakile hare-hare daga 'yan fashin teku na Somaliya shekaru goma da suka gabata.

Yawancin hare-haren da aka kai a shekarun baya-bayan nan dai wasu gungun masu aikata laifuka a Najeriya ne ke kai hare-hare a cikin jiragen ruwa da suka fito daga yankin Delta domin kai farmaki kan jiragen ruwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.