Isa ga babban shafi

'Yan kasuwa sun mutu a tafkin Congo

Akalla mutane shida sun rasa rayukansu, yayin da gommai suka yi batan-dabo bayan kwale-kwalen da ke dauke da su ya kife a Tafkin Kivu da ke gabashin Jamhuriyar Demokuradiyar Congo.

Tafkin Kivu da aka yi hatsarin kwale-kwale a cikinsa.
Tafkin Kivu da aka yi hatsarin kwale-kwale a cikinsa. GettyImages
Talla

Hukumomin kasar sun bayyana cewa, kwale-kwalen ya kife ne a yayin da wani iska mai karfin gaske ke kadawa a Tafkin na Kivu, kuma bayanai na cewa, akasarin fasinjojin ‘yan kasuwa ne dauke da hajojinsu.

‘Yan kasuwar sun taso ne daga garin Mugote da ke yankin kudancin lardin Kivu, inda suka nufi birnin Goma, wato babban birnin Arewacin Kivu.

Daya daga cikin jami’an ‘yan sandan Mugote ya shaida wa manema labarai cewa, kwale-kwalen ya kife ne bayan tafiyar kilomita 20 a cikin tafkin.

Wata majiya ta ce, jumullar fasinjoji 150 suka yi hatsari a cikin wannan kwale-kwalen, amma da dama daga cikinsu sun yi iyo har suka tsiratar da rayukansu.

Ya zuwa yanzu, an tsamo gawarwakin mata uku da kananan yara uku, yayin da ake ci gaba da aikin laluben sauran fasinjojin da suka bace.

Hatsarin jirgin ruwa dai ya zama ruwan dare a Jamhuriyar Demokuradiyar Congo, kasar da ke da karancin hanyoyin zirga-zirgar motoci, abin da ya sa jama’a suka raja’a wajen balaguro a kwale-kwale.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.