An kashe fararen hula 40 a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo
Sama da mutaane 40 ne aka kashe a wasu hare hare da aka kai wasu kauyuka a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo a jiya Juma’a, kamar yadda wasu majiyoyi a yankunan suka bayyana, inda suke zargin ‘yan tsagerar kungiyar CODECO da wannan aika aika.
Wallafawa ranar:
Ana zargin kungiyar ta CODECO da kai hare hare a akalla kauyuka 3 a lardin Ituri, mai kimanin nisan kilomitaa 60 daga shelkwatar lardin, Bunia.
CODECO, na daya daga cikin dimbim kungiyoyi masu dauke da makamai da ke cin karensu babu babbaka a yankin da ke da arzikin albarkatun kasa a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo.
Kungiyar tana ikirarin rajin kare ‘yan kabilar Lendu daga hare haren ‘yan kabilar Hema da kuma sojoji.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu