Isa ga babban shafi

Rwanda da Benin za su hada kai don inganta tsaron kan iyaka

Shugaban Rwanda Paul Kagame ya gana da takwaransa na Jamuriyar Benin Patrice Talon a jiya Asabar, inda ya sha alwashin taimaka masa ta bangaren tsaro don daakile mayaka masu ikkirarin jihadi da ke kwarara arewacin kasar daga iyakarta da Burkina Faso.

Shugaban Rwanda, Paul Kagame (a tsakiya) tare da ministan harkokin wajen Jamhuriyar Benin,  Aurélien Agbenonci a lokacin da ya sauka birnin Cotonou ranar 15 ga Afrilu  2023.
Shugaban Rwanda, Paul Kagame (a tsakiya) tare da ministan harkokin wajen Jamhuriyar Benin, Aurélien Agbenonci a lokacin da ya sauka birnin Cotonou ranar 15 ga Afrilu 2023. AFP - YANICK FOLLY
Talla

Kasashen gabar tekun yammacin Afrika, wato Benin Togo, Ghana da Ivory Coast na ci gaa da damarar tinkarar kalubalen ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi masu shigowa kasashensu daga iyakokinsu na arewa.

A shekarar da ta gabata Benin ta ce tana cikin wata tattaunawa da  Rwanda a game da hadin gwiwar  soji da kayan aiki don dakile ‘yan taa’adda.

A wani taron manema labarai a birnin Cotonou, Kagame ya ce kasarsa a shirye take wajen yin duk mai yiwuwa don kare iyakokin Benin daga ‘yan ta’adda.

Dakarun sojin Benin na fama da matsalar rikicin ta’addanci da ke shigowa arewacin kasar daga Burkina Faso tun daga shekarar 2021.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.