Isa ga babban shafi

Najeriya na bukatar $2.8bn domin yakar zazzabin cizon sauro- Ministan Lafiya

Ministan Lafiyar Najeriya Dr.  Osagie Ehanire ya bayyana cewa ana bukatar dala biliyan 2 da miliyan 800 ($2.8bn) domin yakar zazzabin cizon sauro wato maleriya a kasar har zuwa 2030.  

MInistan lafiyar Najeriya Osagie Ehanire yayin ganawa da manema labarai a Abuja, kan halin da ake ciki kan annobar coronavirus a Najeriya. 2/3/2020.
MInistan lafiyar Najeriya Osagie Ehanire yayin ganawa da manema labarai a Abuja, kan halin da ake ciki kan annobar coronavirus a Najeriya. 2/3/2020. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Ministan wanda Sakataren din-din-din na Ma'aikatar Mamman Mamuda ya wakilta ya bayyana haka ne yayin taron ranar yaki da malariya ta duniya da ya gudana jiya Talata a Abuja, inda ya ce ko a shekarar 2022 da ta gabata an kiyasta cewa Najeriya na iya kashe $1.6bn wurin yakar maleriya.

Ya yi bayani da cewa akalla mutane miliyan 55 ne ke kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro da kuma mutuwar kusan dubu 90,000 masu alaka da zazzabin, a kowace shekara a Najeriya.

Ya kara da cewa, bisa kiyasi kudin da ake kashewa don yakar cutar zai karu zuwa sama da kashi 70, yayin da 'yan Najeriya ke kashe a kalla Naira 2 da dari 280 kan kowane mai cutar zazzabin cizon sauro.....

A cewar sa, nasara shawo kan zazzabin cizon sauro zai inganta lafiya, rage rashin zuwa makaranta, rage fatara tare da saukaka cimma muradun ci gaba mai dorewa.

"saboda haka, dole mu ci gaba da yakar cutar zazzabin cizon sauro zuwa shekarar 2030, bisa tsarin dabarun Hukumar Lafiya ta Duniya". In ji Ministan   

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.