Isa ga babban shafi

Mutane 176 sun mutu a ambaliyar ruwan Congo

Hukumomin Gabashin Jamhuriyar Demokuradiyar Congo sun bayyana cewa, adadain mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa da zabtarewar laka ya kai 176 ya zuwa yanzu.

Zabtarewar kasa ta hallaka mutane 40 a Jamhuriyar Congo
Zabtarewar kasa ta hallaka mutane 40 a Jamhuriyar Congo Reuters/Afolabi Sotunde
Talla

Gwamnan Lardin Kudancin Kivu ya ce, har yanzu akwai dimbin mutanen da suka bace da ba a ji duriyarsu ba kuma ana fargabar laka ta binne su.

Ambaliyar ruwan ta shanye akalla kauyuka biyu da suka hada da Bushushu da Nyamukubi masu makwabtka da Tafkin Kivu a yankin na gabashin Jamhuriyar Demokuradiyar Congo.

Kazalika an samu mummunar zabtarewar laka wadda ta lalata gidajen katako da aka yi musu rufi da karafa.

Kafafen yada labarai na cikin gida sun rawaito cewa, fiye da kashi daya bisa uku na daukacin gidajen yankin, duk ruwa ya yi awon gaba su da suka hada da cibiyoyin kiwon lafiya da makarantu.

A bangare guda, an samu asarar rayukan mutane 130 a Rwanda, tsallaken Tafkin na Kivu sakamakon ambaliyar ruwan da zabtarewar lakar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.