Isa ga babban shafi

Hadarin mota ya kashe mutane 14 da jikkata 68 a Kamaru

Akalla mutane 14 ne suka mutu a kasar Kamaru sakamakon wata mummunar hatsarin mota da wata Bas ta yi a arewa maso gabashin kasar.

Babbar hanyar Kamaru
Babbar hanyar Kamaru RFI/Loïcia Martial
Talla

Cikin wata sanarwa da ya fitar Ministan sufurin kasar Jean Ernest Massena Ngalle Bibehe ya bayyana cewa Hatsarin ya faru ne a ranar Talata a wani kauye mai suna Lom da ke yankin Adamaoua, inda ya ce wani yaro mai shekara 10 na daga cikin wadanda suka mutu.

Wata majiya a wani asibiti da ke kusa da Garoua-Boulai ta ce mutane 68 ne suka jikkata.

Alkaluman Hukumar lafiya ta Duniya sun nuna cewa Kasar Kamaru na daya daga cikin kasashe Afirka dake kan gaba wajen samun yawaitan mace-mace a haduran mota.

A shekarar 2018, kasar dake tsakiyar Afirka ta sami mutuwar sama da mutane 7,000, a haduran ababen hawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.