Isa ga babban shafi

Ana zargin dakarun RSF da ke yaki da sojin Sudan da laifin yi wa mata fyade

Rahotanni da dama da suka bulla a Sudan, sun bayyana yadda dakarun rundunar musamman na RSF ke cin zarafin mata ta hanyar yi musu fyade, lamarin da ya tilasta wa masu rajin kare hakkin dan adam da jami’an lafiya, amfani da kafofin sadarwar zamani wajen gargadin wadanda ke cikin hatsarin fuskantar tashin hankalin. 

Akwai fargabar karuwar cin zarafin kan Mata daga dakarun na RSF.
Akwai fargabar karuwar cin zarafin kan Mata daga dakarun na RSF. REUTERS - ZOHRA BENSEMRA
Talla

Ya zuwa yanzu dai an samu nasarar yada hujjoji da dama ta kafofin sada zumunta kan zarge-zargen da ake yi wa dakarun RSF na aikata fyaden, duk da cewar kungiyoyin farar hula na fuskantar kalubalen yada bayanan, saboda rashin karfin sadarwar intanet a kasar ta Sudan, inda fadan da ake gwabzawa tsakanin dakarun kai daukin gaggawar da kuma sojojin gwamnati ya shiga mako na biyar. 

Abu ne mawuyaci a iya tantance sahihanci rahotannin da ke tuhumar dakarun na RSF kan tafka ta’asar, wadanda wasu bayanai suka ce suna cin zarafin wasu  matan ne a gaban iyalansu. 

Wasu majiyoyi sun ce da fari mata ‘yan kasashen ketare ne ke fuskantar cin zarafin na fyade, amma daga bisani tashin hankalin ya fadada zuwa kan mata ‘yan asalin Sudan. 

Neimat Abubakar Abbas babbar jami’a a kungiyar SIHA da ke kare hakkin mata a yankin kuryar  gabashin Afirka, ta ce suna da tabbas akan rahoton wasu mata akalla 20 da aka yi wa fyade a kudancin birnin Darfur, masifar da tace ta kara yin karfi a Kudancin yankin Darfur, inda ko a watan da ya gabata, sai da aka sace wasu mata akalla 24, tare da  yi musu fyade a wani sansanin ‘yan gudun hijira. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.