Isa ga babban shafi

Buhari na jagorantar bikin kaddamar da matatar man Dangote a Lagos

Yau litinin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke kaddamar da sabuwar matatar man kamfanin Dangote da aka gina a Lagos, wanda ake sa ran ya dinga tace gangar mai dubu 650 kowacce rana domin rage wahalar shigar da tacaccen mai cikin kasar.

Hamshakin attajirin Afirika kuma mamallakin rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote.
Hamshakin attajirin Afirika kuma mamallakin rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote. © Twitter/Dangote Group
Talla

Ana sa ran wannan matata ta dinga tace man fetur da man dizil da kalanzir da kuma man jiragen sama, matakin da ake ganin zai rage matsalolin da ake fuskanta yanzu na rashin samun wadataccen man da ake tacewa a cikin gida. 

Bayanai sun ce a makwanni masu zuwa ake saran kamfanin ya fara aiki gadan gadan a matatar wadda ita ce mafi girma da wani ‘dan kasuwa ya mallaka a nahiyar Afirka, kuma wadda ake sa ran ta samar da kasuwar da ta kai Dala biliyan 21 kowacce shekara wajen sayan danyan mai daga hannun gwamnatin Najeriya. 

Shirin kaddamar da kamfanin gobe ya haifar da matukar farin ciki tsakanin jami’an gwamnati mai barin gado da masu harkar mai da iskar gas da kuma ‘yan Najeriya da dama saboda ci gaban da kamfanin zai samar ta bangaren kasuwanci da kuma ayyukan yi. 

Har ila yau kaddamar da kamfanin na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke kokarin kawo karshen tallafin da take zubawa a bangaren man fetur domin ganin jama’ar kasar sun sayi man a cikin rahusa. 

Alkaluma sun nuna cewar tallafin da gwamnati ke zubawa domin sayar da man da arha a cikin gida ya tashi daga naira miliyan 351 a shekarar 2005 zuwa naira triliyan 4 da biliyan 390 a shekarar 2022.

 A wannan shekara kawai gwamnati ta kasafta kashe naira triliyan 3 da rabi a matsayin kudin tallafin na watanni 6 kawai. 

Hukumar bada lamuni ta duniya IMF ta ce matatar Dangote za ta taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriya idan ta fara aiki gadan gadan, yayin da kungiyar masu sarrafa man ta ce matatar Dangote za ta rage kashi 36 na man da ake shigar da shi Najeriya. 

Shugaban Bankin Raya kasashen Afirka Akinwumi Adeshina yace aikin matatar Dangote shi ne masana’anta mafi girma da nahiyar Afirka ta gani, wadda ya ce za ta amfani kowanne bangare na nahiyar. 

Shugaban kamfanin Dangote, Aliko Dangote ya ce matatar za ta taimaka wajen taskance Dala biliyan 10 na kudaden kasashen ketare da Najeriya ke amfani da shi wajen sayo tacaccen mai da kuma samar da Dala biliyan 10 daga cikin wanda za’a sayar wa kasashen ketare. 

Akalla shugabannin kasashe 5 ake sa ran su halarci bikin na gobe. 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.