Isa ga babban shafi

Yarjejeniya tsagaita wuta ta fara aiki tsakanin bangarorin da ke yakar juna a Sudan

Yau Litinin yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki a tsakanin bangarorin da ke rikici da juna a Sudan, matakin da ke zuwa bayan shiga tsakanin Saudiyya, duk da cewa har zuwa daren jiya an ci gaba da jin karar harbe-harben bindigu da fashewar bama-bamai a Khartoum babban birnin kasar.

Tsinkayen ta sama ga filin jirgin saman Khartum a 20 afrilun  2023.
Tsinkayen ta sama ga filin jirgin saman Khartum a 20 afrilun 2023. © AFP
Talla

A wata sanarwar hadin gwiwa da kasashen Saudiyya da Amurka suka fitar bayan wata tattaunawa a jiyaLahadi, ana sa ran da misalin karfe 9 da mintuna 45 na yau Litinin, yarjejeniyar tsagaita wutar za ta fara aiki har na tsawon kwanaki bakwai tare da fatan tsawaitawa nan gaba.  

Yarjejeniyar da aka cimma a birnin Jidda, a cewar Ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya ta sha bambam da wadanda aka yi ta yi a baya, domin dukkan bangarorin biyu ne suka amince da ita, sannan Amurka da Saudiyya za su sanya ido domin tabbatar da cewa bangarorin biyu ba su saba alkawarin da suka dauka ba. 

Majalisar Dinkin Duniya ta ce yakin na Sudan ya tilasta ficewar kusan mutane dubu 650 daga birnin Khartoum, sannan sama da miliyan daya kuma suka fice daga kasar 

Sai dai har yanzu akwai daidaikun da ke ci gaba da zama a sassan Khartoum duk da hadarin hakan a gare su, fatarsu dai ba ta wuce wannan yarjejeniya ta yi aiki bilhakki da gaskiya ba 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.