Isa ga babban shafi

Bangarorin da ke rikici a Sudan sun amince da tsawaita yarjejeniyar tsagaita

Bangarorin da ke rikici da juna a Sudan sun amince da tsawaita yarjejeniyar tsagaita wutar da ke tsakaninsu zuwa karin kwanaki 5 a nan gaba, sakamakon yadda matakinsu na gaza mutunta yarjejeniyar ya dakile yunkurin jami’an agaji na isar da kayaki ga tarin fararen hular da rikici ya daidaita.

Wani yanki na Sudan bayan tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta a Sudan.
Wani yanki na Sudan bayan tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta a Sudan. AFP - -
Talla

Mazauna arewacin Khartoum sun shaidawa AFP yadda aka rika musayar wuta a jiya litinin gabanin cimma jituwar tsawaita yarjejeniyar, yayinda a bangare guda wasu suka tabbatar da jiyo karar harba makaman atilari daga kudanci birnin ta yadda aka rika ganin hayaki ya turnuke sararin samaniya.

Masu shiga tsakani daga Amurka da Saudi Arabia sun bayyana yadda bangarorin biyu suka kowanne ya karya dokikin yarjejeniyar tsagaita wutar, dalilin da ya hana iya samun nasara a aikin shigar da kayakin agaji ga fararen hular.

Saudiya da Amurka sun bayyana cewa duka bangaren jagoran mulkin Sojan kasar Abdel Fattah al-Burhan da bangaren jagoran sojin RSF Mohamed Hamdan Daglo basu da shirin ja da baya a yakin wanda zuwa yanzu ya salwantar da rayuka dubunnan daruruwan ‘yan Sudan.

Da misalin karfe 7 da mintuna 45 agogon GMT ne yarjejeniyar farkon ta kawo karshe a jiya litinin, dalilin da ya sanya Riyadh da Washington gaggauta sanar da tsawita ta zuwa kwanaki 5 masu zuwa a wani yunkuri na ganin kayakin agaji ya kammala isa ga fararen hula.

Tun bayan nasarar kulla yarjejeniyar a makon jiya, iyalai da dama sun samu damar fita don laluben abinci da ruwan sha duk da cewa farashin kayaki ya ninka fiye da sau 2 idan an kwatanta da farashin yadda ya ke a baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.