MDD za ta zaftare rabin abincin da ta ke bai wa 'yan gudun hijirar Tanzania
Hukumar Samar da Abinci ta Duniya ta ce, nan da watan gobe, za a fara bai wa ‘yan gudun hijira sama da dubu 200 rabin abincin da aka saba ba su a Tanzania sakamakon rashin kudaden tallafi.
Wallafawa ranar:
Zabtarewar abincin wanda shi ne karo na biyu da aka gani a Tanzania cikin watannin baya-bayannan, na zuwa ne bayan dauka makamancin wanann matakin a wasu kasashen duniya dai dai lokacin da Hukumar Samar da Abincin ta Majalisar Dinkin Duniya ke fuskantar matsalar karancin kudi da tsadar farashin kayayyakin abinci sakamakon yakin Ukraine.
Hukumarta ce, tun daga shekarar 2020, aka fara rage yawan abincin da ake bai wa ‘yan gudun hijirar na Tanzania wadanda kashi 70 daga cikinsu, sun fito ne daga Burundi, yayin da sauran kason suka fito daga Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo.
A cikin watan Maris, an rage yawan adadin abincin da ake bai wa ‘yan gudun hijirar daga kashi 80 zuwa kashi 65, yayin da a watan gobe, ake saran adadin zai sake yin kasa zuwa kashi 50 ,lamarin da zai jefa dubban ‘yan gudun hijirar cikin mummunan yanayin fafutukar neman abincin da jikin su ke bukata.
Yanzu haka Hukumar Samar da Abincin ta ce, ana bukatar akalla dala miliyan 21 cikin gaggawa domin kaucewa sake rage adadin abincin na ‘yan gudun hijirar.
An taba daukar irin wannan matakin na rage abincin ‘yan gudun hijirar a kasashen Habasha da Sudan ta Kudu da kuma Kenya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu