Isa ga babban shafi

EU ta tallafawa Nijar da Yuro kusan miliyan 5 domin magance matsalar tsaro

Kungiyar Tarayyar Turai, ta tallafawa Jamhuriyar Nijar da kusan Yuro miliyan biyar, domin siyan makamai da sauran kayayyakin da sojojin kasar ke bukata, domin amfani da su wajen ci gaba da yaki da masu tayar da kayar baya da suka addabi kudu da hamadar Sahara.

Sojojin hadakar da ke karkashin rundunar hadin gwiwa ta MNJTF daga Najeriya da Nijar da kuma Kamaru sun samu nasarar kashe mayakan ISWAP fiye da 100.
Sojojin hadakar da ke karkashin rundunar hadin gwiwa ta MNJTF daga Najeriya da Nijar da kuma Kamaru sun samu nasarar kashe mayakan ISWAP fiye da 100. © ©MNJTF
Talla

An samar da Yuro miliyan 4 da dubu 700 daga cibiyar samar da zaman lafiya ta Turai, wato wani asusu da kasashe mambobin kungiyar EU suka kafa kuma ake amfani da su wajen ba da taimakon soji ga Ukraine, zai ba da gudummawar samar da manyan makamai ga sojojin Nijar, a cewar wata sanarwa da Majalisar EU ta fitar.

Taimakon da ya kai Yuro 297,000 zai kammala tallafin da kasashen Turai ke bayarwa da kuma tabbatar cewa kayan aikin soja da aka baiwa Nijar, ya isa kasar.

Wadannan tallafi biyu sanarwar ta ce, sun kai Yuro miliyan 65 na kudaden da aka baiwa Nijar ta hannun hukumar ta EFF a matsayin wani bangare na dabarun aikin hadaka tare da kungiyar EU da kasashen yankin Sahel kan yadda za ssu kawar da ayyukan ta’addanci.

An samar da cibiyar EFF a watan Maris 2021 don tallafawa harkokin tsaro na waje, a bangaren soji, abin da ya kunshi  gudunmawar kasashe membobin kungiyar, wani shiri da ya kasance mai zaman kansa daga kasafin kudin Turai kuma kasashe mambobin ne kadai ke tafiyar da shirin.

Jamhuriyar Nijar ta zama sansanin sojojin Turai a yankin Sahel bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a Mali da Burkina Faso da ya tilastawa sojojin Faransa da tawagar EU janye wa daga kasashen biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.