Isa ga babban shafi

'Yan tawayen Mali, ba su goyi bayan ficewar dakarun Majalisar dinkin duniya daga kasar ba.

Gamayyar kungiyoyin ‘yan tawaye arewacin Mali sun ce janyewar dakarun kiyaye zaman lafiya na majalisar dinkin duniya daga kasar zai kasance barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankalli a yankin. 

Taron  CSA ta nasu rike da makamai a Kidal Mali,  11 Fabarairun r 2021.
Taron CSA ta nasu rike da makamai a Kidal Mali, 11 Fabarairun r 2021. AFP - SOULEYMANE AG ANARA
Talla

A ranar Juma’ar da ta gabata ce gwamnatin mulkin sojin Mali ta bukaci rundunar kiyaye zaman lafiya ta majalisar dinkin duniya ta fice mata daga kasa ba tare da bata lokaci ba, bukatar da ta biyo bayan tsamin dangantaka tsakanin jagororin gwamnatin sojin kasar da Majalisar dinkin duniya. 

Amma gamayyar kungiyoyin ‘yan tawayen ta ce ficewar dakarun MINUSMA ba tare da wani tsari da zai maye gurbinsu ba zai zama barazana ga tsaro da ci gaban kasar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.