Isa ga babban shafi

Kusan kashi 100 na 'Yan kasar Mali sun zabi sauya kundin mulki - Hukumar Zabe

Hukumar Zaben kasar Mali tace sakamakon wucin gadi ta ya nuna cewa masu kada kuri'a  kasar  sun amince da sauya kundin tsarin mulkin kasar da gagarumin rinjaye.

Katin zaben raba garma kan kundin mulkin kasar Mali.
Katin zaben raba garma kan kundin mulkin kasar Mali. © Sia KAMBOU-AFP/ Montage RFI
Talla

A Lahadin makon jiya ne ‘yan kasar Mali suka kada kuri’ar a zaben raba gardama da hukumomin sojin kasar suka bayyana a matsayin wani mataki mai muhimmaci amsayin hanyar mika mulki ga farar hula.

Sojoji sun mayar da hankali don sauya kundin tsarin mulkin kasar amatsayin wani ginshiki na sake gina kasar Mali, da ke fuskantar kungiyaoyin daban-daban masu dauke da makamai ciki harda masu ikirarin jihadi.

Kashi 97

An bayyana yawan masu jefa kuri'a da kashi 39.4 cikin 100 a kasar da ke kan tudu a yankin Sahel, wadda ke fama da rikicin jihadi da aka shafe shekaru 11 ana yi, amma hukumar zaben kasar tace Kashi 97 cikin 100 na kuri'un raba gardama da aka kada sun amince da sauyin.

Masu adawa da shirin na ganin an yi zaben ne domin baiwa kanar Asimi Goita damar takara a zaben shugaban kasa da aka shirya gudanarwa a watan Fabrairun 2024, duk da cewa tun farko sun yi alkawarin mikawa farar hula bayan zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.