Isa ga babban shafi

'Yan ta'adda sun kashe sojin Burkina Faso da 'yan sa kai sama da 30

Akalla sojojin Burkian Faso 31 da mayakan sa kai 3 ne suka mutu a wani harin da ake zargin mayaka masu ikirarin jihadi ne suka kai musu a  yankin arewacin kasar, kamar yadda majiyoyin tsaro suka bayyana a jiya Talata.

Sojojin kasar Burkina Faso.
Sojojin kasar Burkina Faso. © REUTERS/Luc Gnago
Talla

Zalika, bayan wannan harin, an kashe gwamman mutane a wani farmaki a ranar Litinin, harin baya bayan nan a kasar da ke fama da matsalar mayaka masu ikirarin jihadi da ya  bazu   daga Mali a shekarar 2015.

Da farko dai, wani ayarin da ke jigilar kayan aiki, tare da rakiyar sojoji ne aka wa kwanton bauna a kan hanyarsu ta zuwa Djibo, garin da ‘yan ta’adda suka wa kawanya na tsawon watanni, kamar yadda rundunar sojin kasar ta bayyana.

Ta ce a nan kawai, sama da ‘yan ta’adda 40 ne aka kashe a fadan da aka gwabza, yayin da har yanzu ana neman gwamman sojoji da suka bace bayan rikicin.

Kusan kashi 1 bisa 3  na kasar Burkina Faso  ba ya karkashin ikon gwamnatin Burkina Faso kamar yadda gwamnatin kasar ta sha nanatawa, wanda a dalilin haka ne ma ya sa ta kafa rundunar ‘yan sa kai ta fararen hula da suka kudiri aniyar kare martabar kasarsu.

Mayakan wannan runduna dai su na aiki ne tare da sojoji, inda ayyukansu suka fi ta’allaka ga samar da bayanan sirri.

Sama da mutane dubu 10 da suka hada da fararen hula, sojoji da ‘yan sanda ne suka  mutu tun da aka fara wannan rikicia Burkina Faso, kuma akalla miliyan 2 ne suka daidaita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.