Isa ga babban shafi

Fargaba ta mamaye masarautar Zulu sabida rashin lafiyar sarkin

Rahotanni daga masarautar Zulu a Africa ta kudu, na cewa akwai shakku game da lafiyar sarkin na Zulu, duk da dai kakakin masarautar ya musanta rade-radin cewa an kwantar da sarkin a asibiti.

Sarkin masarautar Zulu Misuzulu kaZwelithini.
Sarkin masarautar Zulu Misuzulu kaZwelithini. AFP - PHILL MAGAKOE
Talla

Basarake Misuzulu Zulu mai shekaru 48 ya dare karagar mulki a bara, bayan mutuwar mahaifinsa Goodwill Zwelithini.

Kafin zaman sa sarki, sai da aka sha rikici game da wanda zai gaji marigayin, kasancewar ‘ya’yan sa da dama sun nuna sha’awar darewa kan karagar mulki, lamarin da raba kan iyalan gidan.

Batun rashin lafiyar tasa ya fito fili ne bayan da Fara ministan masarautar ta Zulu Prince Mangosuthu Buthelezi ya fitar da wata sanarwa, inda a ciki ya ke bayyana fargaba a game da rashin lafiyar sarkin, ya yin da ya jadadda cewa basaraken na kwance a wani asibiti da ke makwafciyar kasar Eswathini.

Ana dai zargin an sanyawa basaraken guba a abinci ne, kasancewar ya fara rashin lafiyar ne, ‘yan kwanaki kadan bayan mutuwar amininsa, wanda ya mutu sakamakon gubar da ya ci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.