Sonko ya bukaci 'yan Senegal su gudanar da gangami gabani jawabin shugaba Sall
Jagoran ‘yan adawar Senegal Ousmane Sonko, ya bukaci al’ummar kasar su fito don yin gangami, a dai-dai lokacin da ake saran shugaban kasar Macky Sall, zai gabatar da jawabin ko zai sake neman wa’adi na uku.
Wallafawa ranar:
Sonko ya ce lokaci ya yi da za su nuna wa Sall bayada hurumin kakabawa al’umma ‘yan takara a zaben shugaban kasar da ke tafe.
A farkon watan Yunin da ya gabata ne, aka yankewa Sonko hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari, bayan samunsa da laifin yin lalata da wata, lamarin da ya haifar da zanga-zangar da tayi sanadin mutuwar mutane 16.
Wannan hukuncin dai, ya haramta masa tsayawa takarar shugabancin kasar a zaben da za’a yi shekara mai zuwa, wanda Sonko ya ce gwamnatin kasar ce ta kitsa hakan, zargin da tuni ita kuma ta karyata.
Da misalin karfe 8 na daren yau Litinin agogon kasar ne, ake saran shugaba Sall ya bayyana matsayarsa ta ko zai tsaya takarar shugabancin kasar a karo na uku.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu