Isa ga babban shafi

Ana fargabar bacewar daruruwan bakin haure a gabar ruwan Spain

Daruruwan bakin haure ne, ciki har da kananan yara ake fargabar sun bace a tsibirin Canary, a cewar hukumomin kasar Spain.

Wani karamin jirgin ruwa da bakin haure suka yi amfani da shi daga kasar Morocco zuwa tsibirin Canary.
Wani karamin jirgin ruwa da bakin haure suka yi amfani da shi daga kasar Morocco zuwa tsibirin Canary. AP - Javier Bauluz
Talla

Jirgin ruwan, wanda ya tashi daga Kafountine, wani yanki da ke kudanccin Senegal mai tazarar kilomita 1,700 daga Tenerife, na dauke da bakin haure akalla 200.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an samu karin wasu jiragen ruwa biyu dauke da gomman mutane da suka bace a gabar ruwan.

Masu aikin ceto na kasa-da-kasa sun shaidawa hukumomin da abin ya shafa cewa, mutanen da aka ceto suna cikin mummunan yanayi, musamman kananan yara.

Tuni rundunar sojin ruwan Spain, ta aike da jiragen sama, domin lalubo wadanda suka bace, yayin da ake hasashen cewa kusan mutum 300 ne suka bace a kananan jiragen ruwan.

A cewar rahoton hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta MDD, akalla bakin haure 559 ne suka bace a shekarar 2022, yayin da ssuke kokarin ketare tsibiran da suke kasar ta Spaniya.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.