Tunisia ta dakatar da albashin malamai sama da dubu 17, saboda matsin tattalin arziki
Mahukunta a Tunusia sun dakatar da biyan albashin malaman makaranta dubu 17 tare da korar wasu shugabanin makarantu 350, matakin da ke zuwa a wani yanayi da matsalolin tattalin arziki suka dabaibaye kasar ta arewacin Afrika.
Wallafawa ranar:
Wannan mataki na gwamnati dai ya shafi akalla kaso 1 bisa 3 na daukacin malaman makarantu da ke Tunisia wanda kuma ake ganin zai sake zafafa kakkarfar zanga-zangar da bangaren ilimi ke ci gaba yi, da ke ganin na daga cikin dalilan da suka sanya gwamnati aiwatar da wannan hukunci.
Malaman makarantu a Tunisa dai sun yi tsayuwar gwamen jaki wajen kin gudanar da aikin baiwa dalibai maki a jarabawar da dalibai suka kammala a a baya-bayan nan.
Cikin dalilan da gwamnatin ta Tunisia ta bayar, sun hadar da mummunan koma bayan da tattalin arzikin kasar ke fuskanta, da ya tilasta gaza iya daukar nauyin malaman.
Tunisia dai na sahun kasashen da ke ganin mummunar tabarbarewar tattalin arziki da hauhawar farashin kayaki sai kuma kamfar abinci baya ga karuwar marasa aikin yi..
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu