Isa ga babban shafi

Yakin Sudan ya raba mutane fiye da miliyan uku da muhallansu-IOM

Kungiyar da ke kula da ‘yan gudun hijira da kaurar baki ta duniya IOM ta ce adadin mutanen da yakin Sudan ya raba da muhallan su ya zarta miliyan 3.

Wasu mata da rikici ya raba da muhallansu a wani sansanin 'yan gudun hijira dake yankin Darfur.
Wasu mata da rikici ya raba da muhallansu a wani sansanin 'yan gudun hijira dake yankin Darfur. ASSOCIATED PRESS - Nasser Nasser
Talla

A wata kididdiga da IOM din ta fitar, ta ce yakin na Sudan na kara muni cikin kowacce rana, dalili kenan da ya sanya adadin ‘yan gudun hijirar ke karuwa.

A cewar kungiyar, a cikin Sudan din akwai fiye da mutane miliyan 2 da dubu dari 4 da suka bar inda suke zuwa wasu sassa, yayin da mutane dubu 730 suka tsallake zuwa makwaftan kasashe.

Tun barkewar yakin tsakanin shugaban gwamnatin sojin kasar Aldelfatah Al-Buhran da mataimakin sa kuma jagoran dakarun RSF Muhammad Hamdan Daglo ne ake ci gaba da samun asarar rayuka da dukiyoyi, yayin da jama’a da dama gudu daga kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.