Isa ga babban shafi

OXFAM ta jadadda rahoton FAO kan yawan mutanen da ke fama da yunwa a Afrika

Kungiyar samar da abinci ta duniya Oxfam ta sake jaddada rahoton hukumar samar da abinci ta majalisar dinkin duniya FAO da ke cewa akalla mutane miliyan 600 ne suke fama da matsananciyar yunwa, yayin da tace wasu karin miliyan 783 zasu iya fadawa halin yunwar nan da 2030 matukar ba’a yi hattara ba.

總部設在英國的人道救援慈善機構樂施會
總部設在英國的人道救援慈善機構樂施會 REUTERS/Peter Nicholls
Talla

Ta cikin wata makala da kungiyar ta Oxfam ta fitar, ta ce duniya ba zata yafewa gwamnatoci ba, matukar suka ci gaba da zura idanuwa biliyoyin mutane na mutuwa saboda yunwa, yayin da su kuma suke rayuwa irin ta alfahari.

A cewar kungiyar bayan gwamnatoci, akwai bukatar masu hannu da shuni su taka muhimmiyar rawa wajen wadata jama’a da abinci, musamman idan aka yi la’akari da irin kazamar ribar da suka rika samu a kasuwancin su lokacin annobar Corona.

Oxfam din tace babu ko tantama a rahoton hukumar abinci ta majalisar dinkin duniyar, idan aka yi duba da irin illar da sauyin yanayi ke zuwa da shi na gurbata kasar noma, da kuma tashe-tsahen hankula da suke raba jama’a da muhallan su ko kuma ma hana manoma zuwa gona.

Bayan zallar yunwar da jama’a musamman a kasashe ‘yan rabbana ka wadata mu ke fama da ita, kananan yara a wasu kasashe na kokawa da rashin abinci mai gina jiki da ke barazanar daukar rayukan su, kuma dukannin alamu na nuna cewa gwamnatoci basa yin abinda ya dace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.