Hukumar (Céni) ta tsawaita da mako guda wa'adin mika takardun takara a DRC
A Jamhuriyar,Demokradiyyar Congo hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (Céni) ta tsawaita da mako guda wa'adin mika takardun tsayawa takara ga mataimakin na kasa a babban zaben da za a gudanar a ranar 20 ga watan Disamba, 2023.
Wallafawa ranar:
A hukumance a jiya asabar ne ya kamata a kawo karshen karbar sunayen yan takara daga hukumar zaben Jamhuriyar,Demokradiyyar Congo.
A karshe dai ofishin hukumar zaben zai ci gaba da kasancewa a bude har zuwa ranar Lahadi 23 ga watan Yulin nan 2023. Duk da cewa a kwanakin baya, shugaban hukumar ta CENI, Denis Kadima, ya yi gargadi karara cewa ba za a yi wani karin wa'adi ba. A ƙarshe, an ba da ƙarin kwanaki bakwai ga 'yan takara na gaba.
Sanarwar da Hukumar zaben kasar na zuwa a wani lokaci da 'yan adawa ke bayyana damuwarsu biyo bayan kisan wani dan majalisa bangaren Moise Katumbi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu