Isa ga babban shafi

'Yan Botswana sun yi zanga-zangar kin jinin dokar sahale auren jinsi

Dubban ‘yan Botswana sun gudanar da wata zanga-zangar adawa da yunkurin majalisar kasar na halasta auren jinsi, inda suka yi dafifi jiya asabar a birnin Gaborone fadar gwamnatin kasar.

Wasu masu zanga-zangar adawa da auren Jinsi.
Wasu masu zanga-zangar adawa da auren Jinsi. AP - Schalk van Zuydam
Talla

Zanga-zangar wadda ta samu goyon bayan kungiyoyin addinai, dubunnan masu boren sun shafe tsawon ranar jiya asabar suna gangamin rike da kwalayen da ke dauke da rubutun nuna adawa da auren na jinsi.

A baya-bayan nan ne majalisar ta Botswana ke kokarin aiwatar da wani hukuncin kotu na shekarar 2019 da ya bai wa masu fafutukar auren na jinsi damar gudanar da auratayyar su, to amma ‘yan kasar su ke ci gaba da bore akai.

Masu boren kusan dukkaninsu na rike da kwalaye ne dauke da rubutun da ke cewa ‘‘Ba mu aminta da auren jinsi ba’’ yayinda wani na daban ke cewa ‘‘dole mu baiwa ‘ya’yan kariya daga auren jinsi’’.

Wani limamin majami’a da ke jagorantar tawaga ta musamman a gangamin na Botswana ya bukaci majalisar kasar ta bayar da damar gudanar da zaben raba gardama kan dokar gabanin aiwatar da ita.

Zanga-zangar ta Botswana na zuwa bayan makamanciyarta a Afrika ta kudu da ke watsi da kudirin bayar da dama ga masu auren na jinsi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.