Isa ga babban shafi

A shirye muke mu dauki matakin soja kan Nijar - Senegal

Senegal ta ce za ta shiga duk wani matakin soji da kungiyar  ECOWAS za ta bada umurni a Jamhuriyar Nijar domin ladabtar da sojojin da suka yi juyin mulki idan bukatar hakan ta taso. 

Wasu sojojin Senegal
Wasu sojojin Senegal REUTERS - ZOHRA BENSEMRA
Talla

 

Ministar Harkokin Wajen Kasar Aissata Tall Sall ta tabbatar da wannan matsayi saboda abin da ta kira matsayin Senegal dangane da kudirorin duniya da ta amince da su, lura da yadda juyin mulkin ke zama ruwan dare. 

Sall ta ce lura da irin wadannan yarjeniyoyi na duniya da Senegal ta amince da su, sojojinta a shirye suke su je Nijar da zaran ECOWAS ta bada umurni. 

Kungiyar ECOWAS ta bai wa Nijar wa’adin kwanaki 7 da ta mayar da zababbiyar gwamnatin Bazoum Mohammed kan karagar mulki, bayan kammala taron shugabanninta da aka yi a karshen makon jiya, inda ta ce rashin daukar wannan mataki na diflomasiya na iya ba ta damar amfani da karfi wajen tilasta shi. 

Yanzu haka manyan hafsoshin tsaron kasashen da ke cikin kungiyar na gudanar da taro a Abuja, domin tsara dabarun da za su yi amfani da su wajen daukar matakin soji idan bukatar hakan ta taso. 

Ministar ta ce kasar Senegal a matsayinta na mamba a kungiyar kasashen ECOWAS, babu yadda za ta kauce wa aiwatar da umurnin kungiyar, yayin da kuma ta amince da cewa, ya zama wajibi a dakile juyin mulkin. 

Dangane da rashin tura sojoji zuwa kasashen Mali da Burkina Faso da kuma Guinea wadanda aka riga yin juyin mulki kuwa, Fall ta ce ECOWAS na tattaunawa da sojojin da suka yi juyin mulki a can domin tsara yadda za a mayar da mulki ga fararen hula. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.