Isa ga babban shafi

Majalisar Najeriya ta yi watsi da bukatar tura sojoji zuwa Nijar

'Yan majalisar dattawan Najeriya sun yi watsi da bukatar shugaba Bola Ahmed Tinubu ta neman izinin tura dakarun kasar zuwa Jamhuriyar Nijar bayan Kungiyar ECOWAS ta ce, za ta yi amfani da karfi domin maido da zababben shugaban kasar da aka yi wa juyin mulki.

Ginin Majalisar Dokokin Najeriya.
Ginin Majalisar Dokokin Najeriya. © Premiumtimes
Talla

'Yan majalisar sun sanar da matsayarsu ce a wani zama da suka gudanar a wannan Asabar, inda suka amince da wani kudiri da ke yin tur da juyin mulkin da aka yi a Jamhuriyar Nijar, yayin da a gefe guda suka jinjina wa shugabannin Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika ECOWAS kan jajircewarsu ta maido da dokokin kundin tsarin mulki a kasar.

Sai dai sanatocin ba su amince da bukatar daukar matakin soji a kasar ba saboda wasu dalilai masu yawa da suka hada da dadaddiyar kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin Najeriya da Nijar.

A maimakon haka, sanatocin sun bukaci shugaba Tinubu da ya kara kaimi ta fuskar zaman sulhu tare da sojojin da suka hambarar da mulkin shugaba Mohamed Bazoum ta hanyar tura wata babbar tawaga zuwa birnin Yamai.

Daga cikin 'yan majalisar akwai wadanda suka bada shawarar sanya dattawan kasar irinsu Obasanjo da Janar Ali Gusau da Abdulsalam Abubakar cikin tawagar domin shiga tattaunawar da sojin na Nijar ta hanyar diflomasiya.

Har ila yau, sanatocin na Najeriya sun kuma kafa hanzarin cewa, sojojin kasar na fama da rashin wadatattun kayan aiki, sannan ba sa cikin shirin shiga wani yaki a daidai lokacin da kasar ke fama da rashin dawwamammen zaman lafiya.

Kazalika sanatocin sun yi amanna cewa, kamata ya yi gwamnatin tarayya ta mayar da hankalinta kan magance rikicin Boko Haram da na 'yan bindiga da na 'yan IPOB masu fafutukar kafa kasar Biafra a maimakon ci gaba da nazari kan kaddamar da farmaki a wata kasa da ke ketare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.