Isa ga babban shafi

AU za ta kafa hukumar tantance kasashen da suka cancanci karbar bashi a Afirka

Hukumar kasashen Afirka AU, ta ce a shekara mai zuwa za  ta kafa tare da kaddamar da fara aikin hukumarta da za ta rika bai wa masu zuba jari bayanai game da bashin da ke kan kasashe da kuma kadarorin da suka mallaka.

Tambarin kungiyar kasashen Afirka AU a harabar hedikwatarta da ke birnin Addis Ababa a kasar Habasha.
Tambarin kungiyar kasashen Afirka AU a harabar hedikwatarta da ke birnin Addis Ababa a kasar Habasha. REUTERS - TIKSA NEGERI
Talla

Wani jami’in kungiyar ta AU ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, babban dalilin daukar matakin shi ne domin kawo karshen rashin adalcin da  hukumomin kasa da kasa ke yi wa kasashen Afirka, wajen bayar da bayanai kan basuka da kadarorin da suka mallaka.

Hukumar gudanarwar AU da wasu shugabannin kasashen Afirka musamman na Ghana da Senegal da Zambia, sun dade suna zargin manyan hukumomin da suka hada da Moody da Fitch da kuma S&P Global, da rashin yi wa kasashen Afirka adalci wajen bayar da rahoton cancantarsu kan karbar bashi, musamman ma a lokacin da suka rika fama da tasirin annobar Korona da ta durkusar da tattalin arzikin duniya.

Sai dai dukkanin manyan hukumomin sun musanta zargin da kasashen na Afirka ke yi musu, inda suka kare kansu da cewar, salo ko tsari iri daya suke bi wajen tantance kasashe a dukkanin nahiyoyin duniya.

A watannin baya, ministocin kudin kasashen Afirka suka cimma matsayar amincewa da kudurin fara shirin kafa hukumar tantance kasashen da suka cancanci zuba hannun jari da karbar basuka a nahiyar, makamancin matakin da ake sa ran majalisar zartaswar kungiyar AU za ta dauka a watan Fabarairun da ke tafe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.