Isa ga babban shafi

Daurin shekaru 7 ya hau kan dan takarar da ya kwararawa shugaban Congo ashar

Kotu a Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo ta yanke wa dan takarar shugaban kasar a jam’iyyar adawa, Jean-Marc Kabund hukuncin daurin shekaru 7 a gidan yari.

Jean-Marc Kabund (daga tsakiya) a birnin Kinshasa.
Jean-Marc Kabund (daga tsakiya) a birnin Kinshasa. AFP - CAROLINE THIRION
Talla

Hukuncin mai tsauri ya hau kan daya daga cikin jagororin ‘yan adawa a Congon ne, bayan samunsa da laifka da dama  ciki kuwa har da kwarara wa shugaban kasar ashar, kamar yadda lauyansa ya bayyana.

Kabund, wanda shi ne tsohon shugaban jam’iyyar Union for Democracy and Social Progress (UDPS), jam’iyyar shugaba Félix Tshisekedi, shi ne kuma tsohon mataimakin shugaban majalisar dokokin kasar.

Tun a ranar 9 ga watan Agusta aka kama Kabund, kuma aka ci gaba da tsare shi a gidan yarin Makala, wanda shi ne kurkuku mafi girma a birnin Kinshasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.